Gungun matasa sun dora daga inda suka tsaya a ranar Lahadi, inda suka ci gaba da nemo rumbunan da aka boye kayan tallafin COVID-19 a Abuja.
Majiyarmu ta rawaito cewa mutane da dama ciki har da matasa sun bude rumbun adana abinci da ke yankin Gwagwalada a Birnin Barayya, Abuja.
- Bata-gari sun yashe rumbunan kamfanoni a Abuja
- An ba wadanda suka saci kayan tallafin Osun sa’o’i 72 su dawo da su
- Abin da ya sa muka boye kayan tallafi —Gwamnoni
- ‘Gwamnati ba ta ce gwamnoni su boye kayan tallafi a rumbuna ba’
Rahotanni sun bayyana cewa matasan sun ci gaba da kwasan kayan tallafi a rukunin masana’antu da ke Idu a Abuja.
A hangi mutane ciki har yara mata da maza suna dibar kayan tallafin da suka hada da shinkafa, taliya da sauran kayayyakin abinci.
A yanzu haka dai mutane na ci gaba da farautar rumbunan da aka boye kayan tallafin annobar COVID-19 a fadin Najeriya.