✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ci direba tarar N26,000 saboda karya dokar COVID-19

Kwamandan FRSC ya ce wannan hukunci zai zama izina ga masu karya dokar COVID-19.

Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Bauchi ta ci tarar wani direban motar haya saboda saba matakan kariyar COVID-19.

Kwamandan Hukumar a Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Kamfanin Dillacin Labarai NAN, a ranar Laraba.

“A wannan karon da COVID-19 ta sake bulla, muna son tabbatar da cewa tashar motoci na bin matakan da NCDC ta kafa.

“Mun kama wata mota da lambar Jihar Legas da ta karya doka wajen diban fasinja fiye da kima.

“An rubuta wa diraben tarar N26,000 saboda rashin ba da tazara da kuma rashin mallakar lasisin tuki.

“Wannan zai zama darasi ga sauran direbobi da ke bijire wa dokokin kariyar COVID-19,” a cewar Abdullahi.

Kwamandan ya jadadda cewa jami’an Hukumar za su ci gaba da kama direbobi masu saba dokokin da aka shimfida na hana yaduwar cutar.