Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), ta ce ta ceto mutum takwas da aka yi safararsu a Jihar Jigawa.
Kwanturolan hukumar a jihar, Mista Ahmed Bagari ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse a ranar Litinin.
- Kotu ta ba da umarnin mayar da Jacob Zuma gidan yari
- KILAF: A Kano za a yi baje kolin fina-finan harsunan Afirka na 5
Ya ce an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ne a ranar Lahadi da misalin karfe 7:00 na dare, inea ma’aikatan hukumar da ke aiki a kan titin Kaya-Daurawa-Roni a Karamar Hukumar Roni ta jihar.
Ya ce wadanda aka ceto, masu shekaru daga 19 zuwa 45, suna kan hanyarsu ta zuwa Kasar Libya da sun tsallaka Jamhuriyar Nijar.
Kwanturolan ya kara da cewa wadanda abin ya shafa sun hada da maza uku da mata biyar, wadanda dukkaninsu sun fito ne daga jihohin Abiya da Edo da kuma Imo.
A cewarsa, mutum daya ne shekaru 45 kawai yana dauke fasfo din Najeriya, inda ya kara da cewa ba a samu wani abu ko kwayoyi a hannunsu ba.
Bagari ya ce babban Kwanturolan NIS, Idris Jere, ya bayar da umarnin mika wadanda abin ya shafa ga Hukumar Hana Fataucin Mutane ta Kasa (NAPTIP), domin ci gaba da gudanar da bincike.
Ya ce, Jere ya shawarci iyaye da sauran jama’a da su daina tura ‘ya’yansu zuwa kasashen waje domin yin aiki.