Jami’an ’yan sada dake aiki da rundunar tsaro ta Operation Puff Adder sun ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su a kusa da garuruwan Namoda da Danbade a Karamar Hukumar Kauran Namoda ta jihar Zamfara.
Rundunar, karkashin jagorancin Baturen ’yan sanda na Kauran Namoda ta ce ta sami nasarar ceto mutanen ne ba tare da wani sharadi ba.
- Kudaden ‘Cryptocurrency’ na taimakawa ta’addanci – CBN
- Taho-mu-gamar ’yan dabar siyasa ta yi sanadiyyar rasa rai a Jigawa
Kakakin Rundunar, SP Muhammad Shehu ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa ranar Lahadi.
Ya ce tuni aka sada dukkan mutanen da iyalansu bayan sun sami kulawar likitoci.
Kazalika, ya ce wata rundunar kuma ta kubutar da shanu 11 da aka yi ittifakin an sace su ne daga Karamar Hukumar Maradun ta jihar.