✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto mutum 2,155 daga hannun ’yan bindigar Zamfara a wata 4

Mutanen da aka ceton sun hada da daliban makarantu da matan aure da kuma kananan yara.

Akalla mutum 2,155 ne aka ceto daga hannun ’yan bindiga da suka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara a cikin wata hudu da suka gabata.

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce mutanen da aka ceto sun hada da daliban makarantun firamare da na sakandare da kuma matan aure da kananan yara.

Kwamishinan Yada Labaran Jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, ya ce “Muna mika jinjinarmu ga sojoji bisa yadda suka kara matsa kaimi a wannan aiki da suke yi,” yana mai cewa an kubutar da mutanen ne a daga watan Satumban 2021 zuwa watan Janairun 2022 da muke ciki

Ya ci gaba da cewa an yi nasarar ceto mutanen ne a sakamakon aikin hadin gwiwar da hukumomin tsaro  wajen yaki da ayyukan ’yan bindiga a jihar.

“Ayyukan da suke yi a Dajin Gando ya sa ’yan bindiga sun ranta a na kare gami da karya lagonsu sosai ta kowace fuska.

“Yanzu muna da kyakkyawar yakini cewa nan ba da jimawa ba za a kawo karshen wadannan ayyukan ta’addanci,” inji Kwamishinan.

A cewarsa, Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, yana aiki kan jiki, kan karfi wajen tabbatar da samuwar zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.

Ya bayyana cewa ko a kwanakin baya, sai da gwamnan ya ziyarci Shugaba Buhari, inda ya yi masa bayanin yanayin tsaron jihar da kuma matakan da gwamantin jihar take dauka domin magance su, ciki har da wata tattaunawa da gwamnan ya yi da Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, wanda kasarsa take da iyaka da Jihar Zamfara.