✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto mutum 16 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna

Sojoji sun bi ’yan bindigar, inda suka yi musayar wuta daga bisani kuma suka kuɓutar da mutanen 16.

Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta sanar da ceto mutum 16 da ’yan bindiga suka sace a Karamar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da darakatan yada labarai na rundunar sojin, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a Yammacin ranar Litinin.

Sanarwar wadda rundunar sojin ta wallafa a shafinta na X, ta ce sojojin sun kuma daƙile yunƙurin wata ƙungiyar ’yan ta’adda na yin garkuwa da mutane.

Manjo Janar Nwachukwu ya ce sojojin da aka tura ƙarƙashin runduna ta ɗaya sun daƙile yunƙurin sace mutane tare da ceto mutanen da aka sace a yankin Tantatu da ke Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.

A cewar sanarwar, sojojin sun kai samamen ne bayan bayanan sirrin da suka samu ranar Lahadi da daddare, lokacin da suka bi sawun ’yan bindigar da suka sace wasu mutane a ƙauyen.

“Da isar su wajen da lamarin ya faru, sojoji sun bi ’yan bindigar, inda suka yi musayar wuta daga bisani kuma suka kuɓutar da mutum 16 da aka sace,” in ji sanarwar.

“Sojojin na ci gaba da gudanar da bincike a cikin dazuka domin ganowa tare da tseratar da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su tare da murƙushe miyagun ayyukan ’yan bindigar.”

Babban Hafsan Sojin Kasa, Taoreed Lagbaja ya yaba wa sojojin kan ƙoƙarin nasu tare da neman su ƙara ƙaimi wajen fatattakar masu aikata ta’addanci.