Rahotanni sun tabbatar da cewa, an ceto wasu mutum 14 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Gauraka da ke Jihar Neja.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, Maryam Yusuf ta ce an samu nasarar ceto mutanen ne sakamakon wani aikin hadin gwiwa na jami’an ’yan sanda da na Hukumar DSS da kuma mafarauta.
- Harin ’Yan bindiga: Mutum takwas sun mutu a Kaduna
- ‘Mutanen Najeriya za su yaba wa Buhari a karshen mulkinsa’
A cewarta, an ceto mutanen 14 ne bayan wani dauki ba dadi na musayar wuta da aka yi tsakanin jami’an tsaron da ’yan bindigar kamar yadda sashen Hausa na Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito.
Ta ce, jami’an tsaron sun kuma samu nasarar tarwatsa sansanin ’yan bindigar da ke yankin Byhazi zuwa Bwari, inda kuma suka kame biyu daga cikin masu satar mutane tare da kwace makamansu ciki had da bindigogi kirar AK-47.
Babu shakka matsalar hare-hare da satar mutane tare da neman kudin fansa ta zama ruwa dare a wasu sassan Jihar Neja, inda a watan Fabrairu ’yan bindiga suka sace gomman dalibai a Makarantar Sakandiren Kimiyya ta Kagara, wadanda aka saka bayan ’yan kwanaki da sace su.
Baya ga Neja, Jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara da Sakkwato, na fuskantar matsalar hare-haren ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane musamman a yankunan karkara.