Kananan yara da sauran mutanen da ’yan bindiga suka sace a yayin da suke tsaka da aiki a wata gona a Jihar Katsina sun kubuta bayan an biyan kudin fasna.
A cikin makon nan ne muka kawo rahoto cewa ’yan bindiga su yi garkuwa da mutum 39 a wata gona, yawancinsu kananan yara a ranar Lahadi — Daga baya shida daga cikinsu suka tsere daga hannun ’yan bindiga.
Sai dai a sanarwar sako su da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta fitar a ranar Asabar, ta ce mutum 21 ne aka sace, sabanin alkaluman da mutanen kauyukan da abin ya shafa suka bayar.
“Muna murnar sanar da cewa an sako daukacin mutum 21 da aka sace su a wata gona a kauyen Mailafiya na Karamar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina.
“An mika su ga iyalansu kuma muna ci gaba da gudanar da bincike,” in ji sanarwar da kakakin rundunar, SP Gambo Isah amma bai yi magana ba game da biyan kudin fansa.
Shi ma da yake tabbatar da sako mutanen, wani mazaunin Mairuwa — kauyen da abin ya fi shafa — ya ce sai da aka biya kudin fansa sannan ’yan bindigar suka sako mutanen.
Ya ce, “An tattauna da su, mai gonar ya ba su N1.5m sannan aka ba su N50,000 na abincin da ’yan bindiga suka ciyar da mutanen — gaba daya dai an biya N1,550,000.”
A cewarsa, wasu shugabannin Fulani a yankin sun shiga cikin lamarin suka roki ’yan bindigar a madadin mutanen kauyukan domin a sako wadanda aka yi garkuwa da su.