’Yan sanda a Jihar Ebonyi sun ceto mutum hudu da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Oshiagu Amia-Ngbo, a Karamar Hukumar Ohaukwu.
Kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Loveth Odah, ta tabbatar da ceto mutanen a ranar Juma’a a garin Abakaliki.
- Kwastam ta kama tabar wiwi na biliyan N1 a Legas
- Za a ci gaba rajistar masu zabe 28 ga watan Yuni —INEC
- Mai larurar tabin hankali ya tashi hankalin masu ibada a Masallacin Harami
- Faransa ta haramta shan giya a bainar jama’a
“Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutanen, amma mun samu nasarar ceto su.
“Ina so na yi amfani da wannan dama wajen jan hankalin mutane da su rika taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri.
“Abun mamaki shi ne yi garkuwa da mai gari da wasu mutum uku, tun karfe 2 na dare amma babu wanda zai sanar da ’yan sanda.
“Amma labari ma fi dadi shi ne am ceto su, kuma na tabbatar za su sanar da ’yan sandan yankin abin da ya faru,”a cewar Odah.
Kazalika, ta ce tilas ne sai mutanen sun taimaka matukar ana so a yaki ta’addanci a jihar.