’Yan Sanda a Jihar Zamfara sun ceto wata jaririya mai wata uku a duniya da wasu mahara suka yi awon gaba da ita.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ayuba Elkanah, ne ya bayyana haka, a wani taron manema labarai a Gusau, a ranar Laraba.
Ya ce an sace jaririyar ce a kauyen Ruggar Tudu da ke Karamar Hukumar Bungudu ta jihar.
Elkanah, ya ce ’yan sandan jihar sun kuma cafke wasu ’yan bindiga uku dauke da miyagun kwayoyi da kuma makamai.
Daga cikin abubuwan da aka samu a wajensu har a baburan hawa, bindigogi kirar AK-47 guda takwas, makamin harba roka guda daya da kuma harsasai.
Da yake karin haske kan ayyukan ’yan sanda a jihar cikin wata hudu da suka shude, kwamishinan ya ce, rundunar ta yi nasara sosai a yakin da take yi da ’yan bindiga, barayin shanu da kuma sauran masu aikata laifuka.
A cewarsa, rundunar ta kwato shanu 69 daga hannu mahara a jihar cikin wata hudun da suka wuce.
Ya kuma sanar da kafa dokar hana amfani da abubuwa masu fashewa ko kara a yayin bukukuwa a fadin jihar.
Don tabbatar da tsaro musamman a lokutan bukukuwan karshen shekara, Elkanah, ya ce rundunar ’yan sandan za ta yi hadin gwuiwa da sauran hukumomin tsaro a jihar don tabbatar da isasshen tsaro.