✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto hafsan sojin da aka yi garkuwa da shi a NDA

Jami'an tsaron da suka ceto shi sun tarwatsa sansanonin ’yan bindiga.

An ceto Manjo Christopher Dantong, hafsan sojin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi a makarantar horas da kananan hafsoshin soji ta NDA.

Hadin gwiwar sojoji da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da sauran hukumomin tsaro ne suka kubutar da Manjo Dantong, a ranar Alhamis, 17 ga Satumba, 2021, bayan sun kashe ’yan bindiga sun kuma tarwatsa sansanoninsu a yankin Afaka zuwa Birnin Gwari na Jihar Kaduna.

Da yake tabbatar da hakan, Daraktan Yada Labaran Runduna ta 1 ta Sojin Kasa ta Najeriya, Kanar Ezindu Idimah, ya ce tuni aka kai Manjo Dantong zuwa NDA  bayan ya samu kulawa daga wani rauni da ya samu.

A cewarsa, za su ci gaba da share yankin har sai sun kamo wadanda suka kashe hafsoshin domin su fuskanci hukunci.

A ranar 24 ga watan Agusta, 2021 ’yan bindiga suka saci jiki suka kutsa cikin harabar NDA da ke yankin Afaka a Jihar Kaduna, inda suka kashe wasu hafsoshin soji biyu, suka kuma yi awon gaba da Manjo Dantong.