✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto giwayen da suka makale tsawon kwana biyu a tabo

Na gode da aikin da kuke yi, kun cancanci yabo

Wani hoton bidiyo ya karade shafin Instagram, wanda ya nuna wasu giwaye sun makale a cikin tabo har na tsawon kwana biyu.

Giwayen sun makale a cikin tabon ne lokacin da suka je wani rafi shan ruwa.

Rafin ya fara kafewa sakamakon yanayin rani da aka shiga a wasu yankunan kasar Kenya.

Sai dai fitar bidiyon ya sa wata kungiyar kare namun daji ta kaddamar da wani gagarumin aikin ceto giwayen biyu.

Intanet na cike da bidiyon iri dabandaban da ke nuna yadda mutane ke taimakon dabbobin da suka makale a jikin wani abu don taimaka musu su koma garkensu ko cikin ’yan uwansu.

A baya-bayan nan an nuna yadda aka ceto wasu giwaye mata guda biyu da suka makale a cikin tabo a kasar Kenya.

Kungiyar ta ce “A kokarin neman ruwan sha, giwaye na fuskantar matsaloli musamman idan rani ya zo, idan suke yawan makalewa a cikin rafin da yake da tabo.

“Saboda yanayin girmansu sukan sha wahala sosai, idan ba a kai musu agaji ba, hakan kan sa da kyar su iya tsira da kansu.”

Kungiyar ta jinjina wa dukkan mutanen da suka taimaka wajen ceto giwayen.

Mutane da yawa sun nuna jin dadinsu kan yadda aka yi aikin ceton inda aka dinga wallafa sakonnin jinjina ga wadanda suka yi aikin ceton a shafin Instgram.

Wani a Instagram ya wallafa cewa, “Na gode da aikin da kuke yi, kun cancanci yabo!”

Wani ma ya wallafa cewa “Sadaukarwa da dagewa, kada ka karaya lokacin da kowa ke tunanin ba za a cim ma nasara ba.”

A ranar Larabar makon jiya ne, wani faifan bidiyo daga Chhattisgarh ya nuna wani yadda wasu giwayen suka bar garkensu da nufin shan ruwa.

Amma aka yi rashin sa’a suka makale, lamarin da ya bar su kwance cikin tabo na kwana biyu kafin a kai musu dauki.