Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta ceto wani yaro mai shekara takwas da aka yi garkuwa da shi.
Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, ya ce an gano yaron ne a Karamar Hukumar Lambata a jihar Neja, inda masu garkuw da shi suka kai shi.
- Gwankin da ya shekara 2 da taya a wuyansa ya shaki iskar ’yanci
- Jaruman Kannywood 7 da shirin ‘Labarina’ ya haska tauraronsu
Ya ce an sace yaron ne ranar 1 ga watan Oktoba, inda wadanda suka sace shi suka bukaci Naira miliyan biyar a matsayin kudin fansa, amma ’yan sanda suke yi nasarar ceto shi bayan sun samu rahoton bacewarsa daga wajen mahaifinsa.
Kazalika, kakakin ya bayyana cewa rundunar ’yan sandan ta cafke wasu mutum biyu da ake zargin su da hannu a garkuwa da karamin yaron, wadanda dukkanninsu ’yan karamar hukumar Lambata ta jihar Neja ne.
“Mutum biyu sun shiga hannu, akwai mai shekara 28 da kuma mai shekara 55 dukkanninsu ’yan asalin Karamar Hukumar Lambata ta Jihar Neja ne,” kamar yadda ya bayyana.
Ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin yana zaune ne a kauyen Chigari na Jihar Adamawa inda ya yi basaja a matsayin manomi, ya sace yaron, ya mika shi ga abokin aikin nasa a Jihar Neja.
Bayan cafke wadanda ake zargin an samu kudi N40,000 a wajensu.
Nguroje, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar ya sa a zurfafa bincike don gano gaskiya tare da rokon jama’a da su ci gaba da ba wa jami’an tsaro hadin kai.