Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da ceto daliban Islamiyya 80 da aka yi garkuwa da su a kauyen Mahuta dake karamar hukumar Dandume a jihar.
Daliban dai sun halarci bikin Maulidi ne a wani kauye da ake kira Unguwar Al-Kasim, yayin da ‘yan bindigar suka musu kofar rago sannan suka yi awon gaba da su.
- An yi garkuwa da daliban Islamiyya da dama a Katsina
- Buhari na ganawa da Daliban Kankara a
- Daliban Kankara na hanyar komawa gida —Gwamnatin Katsina
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar a jihar, SP Gambo Isa ya fitar, inda yace sun samu kiran neman agaji daga baturen ‘yan sanda na Dandume da misalin karfe 10:00 na daren ranar Asabar.
Ya kara da cewa an sanar da su cewa an yi garkuwa da wasu daliban makarantar Hizbur-Rahim Islamiyya dake yankin.
Gambo ya ce, “Akan hanyarsu ta komawa gida daga wajen Maulidin, ‘yan bingidar suka sace, wanda tuni suka sace karin wasu mutane 4 da shanu 12 a kauyen Kauyen Danbaure dake karamar hukumar Funtuwa.
“Ba tare da bata lokaci ba aka tashi rundunar ‘yan sanda ta ‘Operation Sharar Daji’ da ‘yan banga, kuma suka kai musu farmaki har suka yi nasarar ceto daliban gaba daya da wasu 4 da kuma shanu 12 a yayin da suke kokarin tsallake wa da su cikin daji,” inji shi.
Isah ya kara da cewa rundunar na ci gaba da gudanar da bincike a yankin domin cafke wanda suka ji rauni, da kuma wanda suka mutu yayin artabun.