Dominion Okoro, wadda ake zargi da kisan mahaifiyar tsohon Gwamnan Jihar Edo, Maria Igbinedion, ta shiga hannu ’yan sanda suka yi a garin Kalaba na Jihar Kuros Riba.
An kashe Misis Maria Igbinedion ne a ranar 1 ga watan Disamba 2021, kuma ana zargi ’yar aikinta da kashe ta bayan da ta tsere.
- Mutum 1 ya rasu, 70 sun bace bayan ruftawar wurin hakar ma’adinai a Myanmar
- Soumana Boura: Faransa ta kashe jagoran kungiyar IS na Nijar
Wadda ake zargin mai shekara 25 a duniya an cafke ta ne tare da wasu masu laifi mutum 427, kamar yadda Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Phillips Ogbadu, ya sanar.
Ya ce an mika ’yar aikin zuwa kotu don tabbatar da adalci kan laifin da ake tuhumar ta da aikatawa.
Da ta ke zantawa da manema labarai, Dominions ta ce ta shafe shekara daya da wata uku tana yi wa mahaifiyar tsohon gwamnan aiki tare da kula da ita.
“Mukan yi mata tausa ta jiki, lamarin ya faru a ranar 1 ga watan Disamba bayan na gyara mata gado za ta kwanta.
“Na yi yunkurin yi mata satar kudi N100,000 amma sai ta kama ni kuma ta yin min ihun barauniya, ni kuma na dauki kujera na maka mata a kai.
“Ba a jima ba ta fadi a mace, hakan ya sa na kwashi kudin da sauran kayanta na tsere zuwa Kalaba wanda a nan aka kama ni,” a cewar wadda ake zargin.
Sai dai ta ce tun kafin faruwar lamarin akwai wata mata da take rudar ta kan ta yi wa mahaifiyar tsohon gwamnan sata don kula da danta da ba shi da lafiya.
Sai dai kuma dayar ta ki zantawa da manema labarai, bayan shigarta hannun ’yan sanda.