✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke ’Yan Shi’a shida a Abuja

An tarwatsa mambobin kungiyar IMN wadda aka fi sani da Shi’a yayin da a ranar Talata suka gudanar da zanga-zangar neman a saki jagoransu, Sheikh…

An tarwatsa mambobin kungiyar IMN wadda aka fi sani da Shi’a yayin da a ranar Talata suka gudanar da zanga-zangar neman a saki jagoransu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky cikin birnin Abuja.

Mai magana da yawun da rundunar ’yan sandan Abuja, Maryam Yusuf wacce ta tabbatar da ingancin rahoton ta ce an cafke mutum shida daga cikinsu.

Maryam ta ce jami’an ’yan sanda sun fatattaki wadanda suka yi zanga-zangar a gaban Hedikwatar Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Najeriya da ke Maitama a Abuja.

Haka kuma, ta ce wadanda suka shiga hannu za a gurfanar da su a gaban Kuliya da zarar sun kammala gudanar da bincike a kansu.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Litinin ne wata Babbar Kotun Jihar Kaduna ta bayar da umarnin a bai wa matar jagoran mabiya Shi’a a Najeriya, Zeenat El-Zakzaky damar yin jinya a asibiti bayan ta kamu da cutar Coronavirus.

Kotun ta bayar da wannan umarni ga Hukumar Kula da Gidajen Yari reshen Jihar Kaduna bayan lauyan Zeenatu wacce ke tsare a gidan cin sarka, Femi Falana ya gabatar da sakamakon gwajin da ya nuna ta harbu da cutar.

A zamanta na ranar Litinin, kotun ta ce a bai wa Zeenatu damar yin jinya a daya daga cikin asibitocin Gwamnatin Jihar Kaduna kuma wanda yake cikin cikin kwaryar birni.

%d bloggers like this: