An tarwatsa mambobin kungiyar IMN wadda aka fi sani da Shi’a yayin da a ranar Talata suka gudanar da zanga-zangar neman a saki jagoransu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky cikin birnin Abuja.
Mai magana da yawun da rundunar ’yan sandan Abuja, Maryam Yusuf wacce ta tabbatar da ingancin rahoton ta ce an cafke mutum shida daga cikinsu.
- Daraktan Kamfanin Media Trust Alhaji Rabi’u Garba ya riga mu gidan gaskiya
- Gwamnan Benuwai ya kamu da Coronavirus
- Mai Garin da aka sace a Katsina ya kubuta
Maryam ta ce jami’an ’yan sanda sun fatattaki wadanda suka yi zanga-zangar a gaban Hedikwatar Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Najeriya da ke Maitama a Abuja.
Haka kuma, ta ce wadanda suka shiga hannu za a gurfanar da su a gaban Kuliya da zarar sun kammala gudanar da bincike a kansu.
Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Litinin ne wata Babbar Kotun Jihar Kaduna ta bayar da umarnin a bai wa matar jagoran mabiya Shi’a a Najeriya, Zeenat El-Zakzaky damar yin jinya a asibiti bayan ta kamu da cutar Coronavirus.
Kotun ta bayar da wannan umarni ga Hukumar Kula da Gidajen Yari reshen Jihar Kaduna bayan lauyan Zeenatu wacce ke tsare a gidan cin sarka, Femi Falana ya gabatar da sakamakon gwajin da ya nuna ta harbu da cutar.
A zamanta na ranar Litinin, kotun ta ce a bai wa Zeenatu damar yin jinya a daya daga cikin asibitocin Gwamnatin Jihar Kaduna kuma wanda yake cikin cikin kwaryar birni.