✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke ’yan sandan da aka kama suna waya da maharan kurkukun Kuje  

Yanzu haka dai 'yan sandan suna tsare

A halin da ake  ciki, ana tsare da wasu ‘yan sanda biyu bisa dalili mai alaka da harin da aka kai a gidan yarin Kuje, Abuja.

Wata majiya ta shaida mana cewa, “Biyu daga cikin ‘yan bindigar da suka tsere sun kira wani jami’in bincike a daya daga cikin ofisoshinmu….yanzu haka ana kan gudanar da bincike a kansu.”

Aminiya ta tattaro cewa, an damke jami’an ‘yan sanda biyun ne bayan da aka gano sun tuntubi wasu daga cikin wadanda suka tsere yayin harin.

Harin da ‘yan bindiga suka kai gidan yarin a Talatar da ta gabata dai ya yi sanadiyyar tserewar fursunoni sama da 800, ciki har da mayakan Boko Haram da ake tsare da su a kurkukun.

Sa’ilin da ya ziyarci gidan yarin a ranar Laraba don gane wa idanunsa barnar da maharan suka yi, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna takaicinsa dangane da tsarin tattara bayanan sirri na gidan kason.

Shugaban ya ce, “Tsarin tattara bayanan sirrin gidan ya ba ni matukar kunya. Ta yaya ‘yan ta’adda za su shirya, su dauki makamai su kai wa cibiyar tsaro hari sannan su tafi haka? Yaya aka yi tsaron kurkukun ya gaza wajen dakile harin? Fursunoni nawa ne a kurkukun? Mutum nawa ne za ku iya ba da bayani a kansu?”

Buhari ya ci gaba da tambaya cewa, “Jami’ai guda nawa kuke da su? Mutum nawa daga ciki ke dauke da makamai? Shin akwai masu tsaro a kan katanga? Me suka yi? Kyamarorin CCTV?”

Bayan barin Buhari Kuje ne ba da jimawa ba mayakan ISWAP suka dauki alhakin kai mummunan harin.