Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Akwa Ibom ta ce ta cafke mutane 54 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne, kuma tuni wasu daga cikinsu suka amsa laifin da ake zarginsu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, SP Odiko Macdon ya rabawa ‘yan jarida a birnin Uyo ranar Talata.
- Tsadar albasa ta tilasta gwamnan Akwa Ibom ba da umarnin fara nomanta a jihar
- ’Yan jarida 4 sun rasu a hadarin mota a Akwa Ibom
- ’Yan sanda sun yi awon gaba da Basarake kan fadan kungiyar asiri
- Jami’ar Akwa Ibom ta kori malamai 8 kan badala
Ya ce an cafke ‘yan kungiyar asiri 31 a Ibesikpo Asutan, 16 a Oruk Anam, sai 7 a karamar hukumar Etinan na jihar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Biyo bayan mummunan rahoton rikicin kungiyoyin asiri a Obot Idim, Afaha Ikot Obio Nkan, Nung Udoe da Ikot Odongo, a karamar hukumar Ibesikpo Asutan, wanda ya kai ga mutuwar wasu mutane da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne, kwamishinan ‘yan sanda Amiengheme Andrew ya aike da jami’an tsaro domin kwantar da tarzomar.
“An kama mutane 31 da ake zargin ‘yan kungiyar ne., yayin da ake ci gaba da aikin gano sauran masu laifin, sannan ana ci gaba da sanya ido a karamar hukumar don tabbatar da tsaro.
“Kazalika, an cafke wasu mutane 16 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne a karamar hukumar Oruk Anam dangane da rikicin’ yan kungiyar asiri a cikin dangin Inen.
“A wani bangaren na karamar hukumar Etinan, an kuma kama wasu mutane 7 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne.
Ya kuma bayyana cewa an kama wani dalibin makarantar sakandaren Itam ta Yamma mai suna David Okon, wanda ya daba wa wani mai suna Solomon Bassey wuka, wanda suke makarantar daya a rikicin kungiyar asiri tsakanin ‘yan ajin SS2 da SS3.
Sanarwar ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Amiengheme Andrew ya koka kan yadda lalacewar tarbiyya ta kasance a wasu makarantu har ma da al’umma, sannan ya yi kira ga iyaye da su koya wa yaransu dabi’u masu kyau.