’Yan kungiyar IPOB da suka kai hari a ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke Jihar Imo sun shiga hannun ’yan sanda.
Bayan cafke maharan kasa da awa 24 da harin, kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, SP Mike Abattam, ya ce bincikensu ya gano ’yan IPOB ne suka kai harin kuma rundunar tana kokarin kamo ragowar.
- Gwamnatin Borno ta fara shirin daukar sabbin malaman makaranta 3,000
- NAJERIYA A YAU: IPOB Ko Gwamnati: Wa Ke Iko Da Kudancin Najeriya?
SP Mike Abattam ya ce, “Mun bi sawunsu kuma cikin nasara mun cafke mutum uku daga cikinsu.
“Yanzu haka bincike ya yi nisa kuma nan ba da jimawa ba ragowar ma za su shiga hannu,” in ji shi.
Tun da farko jami’in ya ce rundunar tana “Zargin IPOB ce a kai harin, saboda bincikenmu ya nuna mana hakan, kuma muna da alhakin bincike kan duk wanda muke zargi.”
Aminiya ta ruwaito yadda wasu mahara da sanyin safiyar ranar Litinin suka kai hari hedikwatar INEC da ke Jihar Imo, inda suka kashe masu gadi suka kona abubuwan amfani masu tarin yawa.
IPOB dai na ci gaba da kai hare-hare ofishoshin INEC, a wani yunkuri na hana mutane shiga zaben 2023 da ke tafe.