Jami’an tsaro a yankin Agadas da ke Jamhuriyar Nijar sun tsare Mai Garin Fashi, Sharou Sanda, bayan sun gano hodar Iblis mai nauyin kilogram sama da 200 a cikin motarsa.
Ana zargi mai garin ne da jigilar hodar Ibilis din zuwa wani yanki, amma kafin su isa shi da direbansa suka fada a komar jami’an tsaro.
An dai kiyasta cewa, darajar hodar Iblis din da aka kama Sharou Sanda da ita ta kai biliyan biyar na kudin CFA.
Ya zuwa yanzu ’yan sanda na tsare da mai garin tare da direbansa, a yayin da ake ci gaba da neman wani mutun da ya hada baki da su.
Bayanai sun nuna cewa an tisa keyar Sharou Sanda da direbansa zuwa birnin Yamai, babban birnin kasar ta Jamhuriyar Nijar domin gudanar da zuzzurfan bincike.
Ko a ranar 7 ga watan Disamban 2021, sai da Hukumar Yaki da Sha da Ta’ammuli da Miyagun Kwayoyi ta Jamhuriyar Nijar ta kama sama da kilogram 330 na tabar wiwi tare da cafke wasu mutun 10.