✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke shi kan satar dan kamfan mata

An kama shi yana sanye da wasu daga cikin dan kamfan mata da ya sace

Dubun wani mutum da ake zargi kan satar dan kamfan mata ta cika a garin Ilori na Jihar Kwara.
An kama wanda ake zargi da sace wa mata dan kamfan ne sanye da wasu daga cikinsu da kuma guraye da layoyi.

“A yayin bincike, ’yan sanda sun gano yana sanye da dan kamfan mata guda biyu, sannan ya daura guraye da layoyi da wasu kayan tsubbace-tsubbace a cikin leda,” in ji karar da ’yan sandan suka gabatar wa kotun.

Dan sanda mai gabatar da kara, Ayeni Gbenga, ya ce mutumin ya shaida wa ’yan sanda cewa, “ya kwashe kamfan matan ne a kan igiyar shanya kuma zai yi amfani da su ne domin yin tsafi.”

Ya kara da cewa wanda ake zargin ya kuma yi yunkurin tserewa daga wurin da ’yan sanda suka tsare shi.

Don haka ya bukaci kotun da ta tsare shi, kuma Mai Shari’a Gbadeyan Kamson na Kotun Majistare da ke Ilori, ya ba da umarnin a tsare shi a Gidan Yarin Gwamnatin Tarayya da ke Mandala.

Kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Maris, 2023.