Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta kama wasu mutum shida a kan zargin kashe wani mutum da aka yi a wajen sayar da abinci a Legas.
A ranar Juma’a 11 ga watan Satumba ce wani mutum ya harbe Kayode Oloruntoba bayan gardamar da ta kaure tsakaninsu kan wanda za a fara sayar wa da shawarma a cikinsu unguwar Werewere da ke yankin Alagbado.
Zuwa yanzu dai wanda ya yi harbin ya tsere amma ana neman shi ruwa a jallo.
A cewar mai magana da yawun rundunar, SP Olumuyiwa Adejobi, lamarin ya auku ne da misalin karfe 9:30 na dare a lokacin da gardama da kaure a tsakanin marigayin da wanda ya harbe shi.
Ya ce a gaban abokin marigayin mai suna Okikiola Kazeem lamarin ya faru, amma ya ki ya kai rahoto ga ‘yan sanda sai ya dauke shi ya kai shi wajen wani mai maganin gargajiya a Jihar Ogun domin ya cire masa harsashin bindigar.
Kakakin ya ce, “Daga baya ya kai dan uwan abokin nasa wajen mai maganin gargajiyar inda daga bisani ya mutu a can sakamakon raunin da ya samu daga harbin bindigar.
“Yanzu haka Kwamishinan ‘Yan sandan Legas CP Hakeem Odumosu ya ba da umarnin kamo wanda ake zargin da hannu a kisan.
“An kuma kame mutum shida da aka fara bincike a kansu wadanda suka hadar da abokin marigayin wanda ya shaida faruwar lamarin, Okikiola Kazeem, wanda shi ya gayyaci marigayin zuwa inda ake sayar da shawarma.
“Sai mai gidan abincin da ake sayar da shawarmar mai suna Chimezie Amaechi, da kuma manajan gidan abincin na ‘Avid’, Olayinka Oyedokun, sai Femi Victor da Taiwo Morokola da kuma Omole Wasiu”, inji shi.
Ya ce wadanda aka kame suna bai wa ‘yan sandan muhimman bayanai.
Ya kuma ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar ya ba da umarnin a binciki lamarin a Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na rundunar da ke yankin Yaba.