✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke mutum 9 da ake zargin ’yan fashi ne a Jigawa

Rundunar ’yan sandan Jigawa ta damke wasu mutum tara da ake zargin manyan ’yan fashi da suka addabi yankin karamar hukumar Babura da ke arewacin…

Rundunar ’yan sandan Jigawa ta damke wasu mutum tara da ake zargin manyan ’yan fashi da suka addabi yankin karamar hukumar Babura da ke arewacin jihar.

’Yan sandan sun ce sun yi nasarar kame mutanen ne a daidai lokacin da suka kai hari a kauyen Andau suka yi wa wasu mutane fashin baburan hawa har guda uku kuma suka harbe wani matashi mai suna Khamisu Idris  har lahira.

Lokacin da ’yan sanda suka samu labarin abin da yake faruwa ne suka kai wa wadanda ake yi wa fashin gudunmawa.

Da ganin ’yansandan sai ’yan fashin suka bude musu wuta, amma ba su yi sa’ar harbin dan sanda ko daya ba.

Da wuta ta wuta sai maharani suka watsar da baburan suka taka a guje, inji ’yan sandan.

A lokacin da suka tsere dai sun bar bindiga kirar AK47 da albarusai tara.