Jami’an ’yan sanda a Jihar Neja a ranar Alhamis sun yi nasarar cafke wasu mutane tara da ake zargi da aikata fashi da makami a jihar.
A cewar kakakin rundunar a jihar, DSP Wasiu Abiodun, An kama dukkan mutanen ne a wurare daban-daban kuma an yi nasarar kwato manyan motoci shida a hannunsu.
- ’Yan bindiga sun kai hari Asibiti a Kaduna, sun sace ma’aikata
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 45 a Zamfara
- Ya auri kanwarsa da ta bace tun tana jaririya
Ana zargin mutanen ne da hannu a wani fashi da aka yi a Minna, babban birnin jihar a kwanakin baya.
Kazalika, an kama wasu daga cikin wadanda ake zargin da karbar motocin sata, sai kuma wani da aka kama shi da bindiga kirar pistol.
Kakakin ’yan sandan ya ce tuni jami’ansu suka dauki mataki a lokacin da aka gabatar musu da korafi kan ’yan fashin bayan sun kai hari unguwar Farm Centre dake Minna, inda suka yi awon-gaba da motoci shida a yankin Niteco da Tunga da kuma Bidda.
An dai kama wadanda ake zargin ne a Babban Birnin Tarayya Abuja da Bidda da Minna da kuma jihar Sakkwato.