Hukumar Tsaro ta NSCDC ta kama mutum 14 da ake zargi da yin fyade da wasu da aka zarga da satar kayan na’urar rarraba wutar lantarki biyu a Jihar Kaduna.
Kwamnadan NSCDC a jihar, Nuradeen Abdullahi shi ne ya sanar da hakan a yayin tattaunawa da ‘yan jarida a ranar Talata.
- An kama masu fyade 40 a Katsina
- Matsafa sun yi wa ’yar shekara 13 fyade
- Yadda mahaifina ya yi min fyade
A cewarsa, “Daga 1 ga watan Oktoban 2020, mun kama masu fyade 14 da kuma masu aikata wasu laifuka daban-daban.
“An kama mutum biyu bisa zargin safarar kwayoyi ranar 6 ga watan Oktoba, sai mutum biyu da ake zargi da fasa na’urar rarraba wutar lantarki a ranar 25 ga watan Oktoba da sai wani da aka zarge shi da satar karafan jirgin kasa ranar 13 ga watan Oktoba”, inji shi.
Abdullahi ya ce wasu masu laifukan an kai su kotu domin tantancewa, kafin ma’aikatar shari’ar jiha ta bada shawarwari.
“Muna godiya da taimakon da kwamishinan walwalar jama’a da Kungiyar Lauyoyin Mata da kungiyar sa’ido ta Kaduna suka bayar wajen kamen da aka yi,” inji shi.
Ya kuma kira ga iyaye su kula da ‘yayansu tare da sanin abokan su da duk wuraren da suke zuwa.