An tsare wasu mutum uku bisa zargin su da kone gida Sarkin Fulani Adamu Oloru da kuma Kasuwar Kara a Jihar Ogun.
A ranar Litinin wasu, ’yan daba suka kai wa al’ummar Fulani hari inda suka kone gidan Sarkin Fulanin da kuma kasuwar a harin kin jinin Fulani da Sunday Adeyemo (Sunday Igboho) ke jagoranta.
- Abin da ’yan bindigar Zamfara suka fada min —Sheikh Gumi
- Dalilin da ya sa ake tsoron aurenmu —Mata ’Yan Boko
- Ya mutu bayan dirowa daga bene mai hawa 7 a kokarin tsere wa jami’an EFCC
A harin wanda ke shan la’anta daga bangarori da dama ne aka kashe wani mai suna Alhaji Jiji aka kuma kashe shanun Fulani da dama a yankin Yewa.
A ranar Juma’a, Kakakin ’Yan Sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya ce an kama mutum uku da ake zargi da hannu a aika-aikan, sannan, “Shugabannni, shawararta da iyayen gidan ’yan dabar ma za su shiga hannu domin su fuskanci hukunci” don ya zama darasi ga wasu.
“Rundunar ’Yan Sadan Jihar Ogun na kira ga mautanen jihar su hada kai da jami’an tsaro don wanzar da zaman lafiya tsakanin ’yan Najeriya a Jihar.”
Ya kara da cewa a kwanaki ukun da suka gabata an kai hare-hare a kan al’ummomin Fulani da ko a doka “sun cika shika-shikan zama Yarabawa.”
Ya ce mutanen da aka kai wa harin sun fi shekara 20 da fara zama a yankunan da yawanci Fulani ne da aka haifa suka taso a yankunan, suna kuma jin Yarabanci kamar kowane Bayarabe.
“Don haka ba kuskure ne a doka a hana wani dan Najeriya ’yancinsa na zama a duk yankin kasar domin neman halaliyarsa, har da kiwon shanu.
“Yana kuma da kyau makiyaya su guji yin barna a gonaki domin hakan ke zama musabbabin rikici tsakaninsu da manoma ’yan asalin yankunan.”
Kakakin ’yan sandan ya roki makiyaya a yankin na Yewa da su fallasa bata-garin cikinsu da ke “yawan haifar da tashin-tashina a tsakaninsu tare da gurgunta zaman lafiya tsakanin al’umma.”