’Yan sanda a jihar Kebbi sun cafke wasu mutum uku da ake zargi da dillacin makamai ga ’yan bindiga a jihar.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Nafi’u Abubakar ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Litinin.
- Yadda Rikadawa ya martaba yaronsa da auren ’yar cikinsa
- El-Rufai ga Gumi: Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba
- Ali Jita: Kannywood ta girgiza da rasuwar mahaifinsa
- Za mu shirya mukabala tsakanin Abduljabbar da Malamai — Ganduje
“A ranar 27 ga Janairu 2021, jami’anmu sun cafke wani mutum a yankin Malando-Garin-Baka, da bindigu guda hudu.
“Yayin da ake tambayarsa game da bindigun bai bada gamsashiyar amsa ba, don haka ana ci gaba da tsare shi,” a cewar Abubakar.
Kazalika, ya ce sun sake cafke wasu mutum biyu masu alaka da mutumin da aka kama da makaman kuma bincike ya tabbatar suna zaune ne a gida daya.
Haka kuma ya ce bayan gudanar da bincike, rundunar ’yan sandan jihar ta gano cewa ababen zargin na yi wa bata gari fataucin makamai.
A dalilin haka Kakakin ya ce rundunarsu za ta gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu da zarar sun kammala bincike domin a yanke musu hukuncin da ya dace daidai da abin da suka aikata.
Ya kara da cewa, Kwamishinan ’yan sandan jihar, Adeleke Adeyunka-Bode ya ja hankalin jama’ar jihar da su rika taimaka wa da jami’an tsaro da bayanan sirri da za su taimaka wajen magance matsalar tsaro.
“Kwamishinan ya ja hankalin mutanen da su kasance masu bin doka, sannan su ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro da bayanan tona asirin masu aikata laifuka,” in ji Kakakin.