✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke matashin da ya kashe mahaifiyarsa a Kano

Matashin ya amsa wa ’yan sanda cewa shi ne ya kashe mahaifiyarsa kuma yana yin fataucin miyagun kwayoyi

Matashin nan da ya caka wa mahaifiyarsa wuka ya kashe ta a Jihar Kano ya shiga hannun ’yan sanda.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito kakakin ya ruwaito kakakin ’yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, yana cewa, “Matashin ya amsa abin da ake zargin ya aikata da kuma yin fataucin miyagun kwayoyi.”

Matashin mai shekara 22 ya kashe mahaifiyar tasa mai shekaru 50 ne ta hanyar sossoka mata wuka a sassan jikinta, saboda wata sabani da suka samu.

Daga nan ya cika wandonsa da iska, kafin makwabta su shiga su same ta kwance cikin jini, su garzaya da ita asibiti.

Aminiya ta ruwaito cewa matashin, wanda ake wa lakabi da Kwarangwal, ya yi wannan aika-aika ne a unguwar Rimin Kebe da ke Karamar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano.

NAN ya ruwaito kakakin ’yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, yana cewa rundunar ta yi nasarar cafke matashin a wata maboyar bata-gari da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa ta jihar.

Yadda abin ya faru

Yayarsa ta bayyana cewa, “Ya fi shekara rabonsa da zuwa inda muke, kwatsam sai muka ga ya shigo da misalin 5:30 ba yamma.

“Ya koma wurin mahaifinsa da zama a unguwar Kurna tun bayan da ya samu tabin hankali da har yanzu ba a tantance gaskiyar ba.

“Da shigarsa ya tambaya ina take, amma a lokacin ba a nan, amma ya ce a kira ta, tunda gidan makwabta ta je.

“Da shigowarta cikin farin ciki ta yi mishi maraba, ni kuma ina jin su; tana bude daki sai na ji ta yi ihu, nin kuma ina fitowa sai na gan shi da wuka.

“Ya yi kokarin kawo min hari amma na tsere, shi ne jama’a suka taru saboda yadda suka ga yana tafiya akwai alamar tambaya. A waje ya jefar da wukar ya gudu.

“Ita (marigayiywar) takan je ta duba shi lokaci-lokaci. Zuwanta na karshe, a cikin watan Ramadan ne, kuma a lokacin ma koro ta ya yi, sai aka rirrike shi, ta shige wani daki ta boye.”