An cako wani wani matashi mai shekara 27 da ake zargi da kashe tsohon mai gidansa a Jihar Nasarawa.
Ana zargin matashin ya hallaka tsohon da ya dauke shi aiki a karkashinsa mai suna Martins Omeri, Mataimaki Babban Mai Binciken Kudi a Ofishin Babban Akanta na Kasa da ke Abuja.
Mamacin na zaune da iyalansa ne a rukunin gidajen sojojin ruwa da ke Karshi, Karamar Hukumar Karu da ke Jihar Nasarawa.
- Dan takara ya yi martani kan zanga-zangar adawa da aka yi masa a jihar Kano
- Balahirar Fyade: Jan hankali ga iyaye da al’umma (3)
- An kama shi da kokunan kan dan Adam
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Ramhan Nansel ya ce da misalin karfe 11:45, ’yan sandan da ke Karshi, sun gudanar da tsattsauran bincike inda suka cafke wanda ake zargi da aikata laifin a yankin Arab a Abuja.
“An gudanar da bincike a gidansa inda aka ci karo da wasu kayayyaki mallakar wanda aka kashe a matsayin hujja.
“Kayan sun hada da waya kirar Infinix, kwamfuta laptop, tufafi, takalma, na’urar aski da wasu sauran kayayyaki.
“Wanda ake zargi ya samu rudewar tunani ce wa ya salula cikin gidan mamacin da tsakar dare ranar 17, ga watan Nuwambar, 2020 yayin da yake kwance yana barci, ya samu ya kashe shi ta hanyar amfani da wani katakon kofa da aka samu a jikin mamacin a ranar 19, ga watan Nuwambar, 2020”.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Bola Longe ya bayar da umarnin mayar da binciken ake wa wanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar da ke Lafia don fadada bincike da gurfanar da shi a kotu.
Nansel ya ce, ya yi kira ga mutanen gari da ’yan uwan mamacin da su rika lura sosai kan mutanen da za su rika dauka aiki suna kai su gidajensu gudun faruwar irin hakan a nan gaba.