Wata Kotun Majistare a Kaduna ta tsare wasu mutum biyu a gidan yari bisa zargin mallakar bindigogi ta haramtacciyar hanya.
Yayin zaman kotun a ranar Laraba, Alkali Ibrahim Emmanuel, ya ba ba umarnin a tsare wadanda ake zargin kafin kotun ta samu shawara daga Darakatan sashen tuhuma na jihar.
- An kama mai gyaran wuta a cikin likitocin bogi masu aiki a asibitoci fiye da 100 a Kano
- Zan amince da nasarar Binani muddin ta kada ni a mazabarta —Ardo
Da farko dan sanda mai tuhuma, Sufeto Sunday Baba, ya shaida wa kotun an cafke wadanda ake zargin ne a watan Disamba a unguwar Rigasa suna dauke da bindigogi kirar gida da adduna da wukake.
Ya ce sun yi ikirarin za su kai makaman ne ga ubangidansu a matsayin kayan aikin fashi da makami.
Ya kara da cewa, har yanzu ’yan sanda suna farautar ubangidan nasu wanda ya yi layar zana.
Kotun ta ki karbar rokon wadanda ake tuhumar, sannan Alkalin ya dage shairi’ar zuwa 6 ga Fabrairu.
(NAN)