✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke masu yi wa ’yan bindiga safarar makamai a Kaduna

Dubunsu ta cika a kan hanyarsu ta kai wa ’yan bindiga makamai a Zariya

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kwace bindigogi da albarusai 344 tare da  kama wasu mutum biyu da take zargi da yi wa ’yan bindiga safarar makamai a jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya sanar a ranar Lahadi cewa jami’ansu da ke sintiri a yankin Kwarkwaron Manu a unguwar Basawa da ke Zariya ne suka cafke mutanen.

A cewarsa, daya daga cikin wadanda ake zargin ya gudu a lokacin da ’yan sanda suka tsayar da su domin a bincike su.

Yayin da ake bincikar babur dinsu an gano bindiga kirar AK47, kunshin harsashi guda 344, wayoyin hannu guda 10 da kuma wata laya guda daya.

Daya daga cikin wadanda ake zargi, ya bayyana cewa shi da abokinsa na kan hanyarsu ta yi wa wasu ’yan bindiga safarar makaman ne.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ya bayar da umarnin gudanar da bincike don gano inda za su kai makaman da kuma kamo wadanda za a kai wa.

Rundunar ta kara tabbatar wa da jama’a kokarinta na kawar da masu aikata laifuka a fadin jihar.