Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kwace bindigogi da albarusai 344 tare da kama wasu mutum biyu da take zargi da yi wa ’yan bindiga safarar makamai a jihar.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya sanar a ranar Lahadi cewa jami’ansu da ke sintiri a yankin Kwarkwaron Manu a unguwar Basawa da ke Zariya ne suka cafke mutanen.
- Tankar gas ta yi bindiga, mutum 9 sun mutu 40 sun jikkata a Afrika Ta Kudu
- EFCC ta yi gwanjon kadarorin su Diezani a kasuwa
A cewarsa, daya daga cikin wadanda ake zargin ya gudu a lokacin da ’yan sanda suka tsayar da su domin a bincike su.
Yayin da ake bincikar babur dinsu an gano bindiga kirar AK47, kunshin harsashi guda 344, wayoyin hannu guda 10 da kuma wata laya guda daya.
Daya daga cikin wadanda ake zargi, ya bayyana cewa shi da abokinsa na kan hanyarsu ta yi wa wasu ’yan bindiga safarar makaman ne.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ya bayar da umarnin gudanar da bincike don gano inda za su kai makaman da kuma kamo wadanda za a kai wa.
Rundunar ta kara tabbatar wa da jama’a kokarinta na kawar da masu aikata laifuka a fadin jihar.