Wasu mutum shida da ke yi wa ’yan bindiga leken asiri a Jihar Neja sun shiga hannu.
Dubun masu yi wa ’yan bindigar leken asirin ta cika ne a lokacin da suke kokarin kai wa iyayen gidansu bayanai kan ayyukan sojoji a Kananan Hukumomin Munya da Shiroro na Jihar.
- An kai wa unguwar Hausawa hari a Imo
- Matsalar tsaro: Sarkin Zazzau ya yaba wa al’umma kan kare kansu
- Sojoji sun ragargaji ’yan Boko Haram a Gwoza
- Hada-hadar kudaden Cryptocurrency haramun ce —Sheik Bin Usman
Jami’an tsaro sun damke mutanen ne a yayin da hare-haren ’yan bindiga ke ci gaba da addabar jihar.
Daga cikin mutanen da asirin nasu ya tonu akwai wani likita da manoma da wasu matasa.
Wata majiyar tsaro ta tabbatar wa Aminiya cewa mutanen na hannun ’yan sanda ana bincike domin gano hakikanin alakarsu da ’yan bindiga.
Aminiya ta nemi samun karin haske daga mai magana da yawun ’yan sanda an Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, amma wayarsa a kashe, har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoto.
Hakan kuma nan zuwa ne a daidai lokacin da Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Gabashin Jihar, Sanata Mohammed Sani Musa ke cewa sama da al’ummmomi 42 na Jihar na karkashin ikon kungiyar Boko Haram.