Jami’an tsaro a kasar Belgium sun tusa keyar wasu ’yan masu tsaurin ra’ayi ’yan kasar Denmark da ke shirin kona Al-Kur’ani.
An cafke shida daga cikin masu tsaurin ra’ayin aka kuma kore su daga kasar saboda aniyarsu ta tunzura Musulmin Belgium.
Mutanen’yan kungiyar Stram Kurs ce wadda wani dan tawaye mai yakar Mususlunci da ’yan gugun hijira, Rasmus Paludan ke jagoranta.
Shafin Stram Kurs ya ce an tsare Paludan a Faransa aka kuma kore shi daga Belgium.
Stram Kurs ta yi kaurin suna wurin tunzura jama’a a yankin Scandinavia kuma hukumomin Belgium sun yi amannar tana shirin kona Al’Kur’ani ne a unguwar Molenbeek da ke birnin Brussels, wanda yawancin mazaunansa Musulmai ne ’yan asalin kasar Morocco.
‘Barazana ga zaman lafiya’
Wata majiya mai kusanci da binciken ta shaida wa kamfanin dillancin labaru na AFP cewa ’yan sanda sun shigar da kara kan yunkurin kona Al-Kur’anin ga ofishin babban mai gabatar da kara da ke Brussels.
Sakaraten Ma’aikatar kula da masu neman mafaka da gudunin hijiri na Belgium, Sammy Mahdi wanda dan asarin kasar Iraqi ne ya yi maraba da tsare mutanen da aka yi.
“An umarce su da su gaggauta ficewa daga Belgium kuma sun bar kasar”, inji ofishin.
“An hana su izinin zama saboda su babbar barazana ce ga zaman lafiyar kasar Belgium.
“A baya-bayan nan an sake tsare wani mutum a Faransa saboda wannan yunkurin”, inji shi.
“Jamus ta dauki makamancin matakin a kan mutum wanda jami’an tsaro ke wa kallon mai yada kiyayya”, inji sanarwar amma ba ta ambaci sunan Paludan ba.
A watan Agusta fada ta kaure a garin Malmo da ke Kudancin Sweden bayan masu tsaurin ra’ayi sun kona Al-Kur’ani, lamarin da harzuka mazauna suka yi zanga-zanga tare da auka wa ’yan sanda da raunata da dama daga cikinsu.
Yada kyamar Musulmi a Belgium
Da farko ana sa ran Paludan, wanda lauya ne da ke zauna a Denmkark zai halarci taron, amma kasar Sweden ta hana shi shiga kasar.
“Ba ma bukatar masu zuwa su yada kiyayya a tsakanin al’ummominmu da dama can kansu na rabe”, inji Mahdi.
“Ban damu da bangaren da mutum ya fito ba, damuwata ita ce zaman lafiyar ’yan kasa”, inji shi.
A ranar 30 ga watan Oktoba, Paludan ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ya sanar da karamin ofishin jakadancin Faransa da ke Copenhagen shirinsa na kona Al-Kur’ani a Arc de Triomphe da ke binin Paris a ranar 11 ga watan Nuwamba.