✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke masu garkuwa da mahaifin tsohon Gwamnan Filato

Wanda ake zargin sun kware wajen sayar da makamai ga masu laifi.

’Yan Sanda sun cafke mutum takwas da suka sace suka kuma kashe Mista Defwan Dariye mai shekara 93, mahaifin tshohon Gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Frank Mba ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa wadanda ake zargin sun sace dattijon sun tsare shi tsawon kwana takwas, alhali yana fama da rashin lafiya.

A cewarsa, bayan tattaunawa mai tsawo, an biya masu garkuwar kudin fansa Naira miliyan 10, amma maimakon su sake shi, sai suka kashe shi.

Bayan sun jefar da gawar mamacin da suka sace a watan Yunin 2020, a wani waje an gano ta, jami’an tsaro kuma suka shiga bincike.

“A kwana 30 da suka gabata, ’yan sanda sun samu gagarumar nasarar cafke mutum takwas kan zargi da taka muhimmiyar rawa a garkuwa da kuma kashe mahaifin tsohon gwamnan.

“Wadanda ake zargin, dukkansu — inda kadan daga cikinsu — ’yan kauye daya da marigayrin a Karamar Hukumar Bokkos,” inji shi.

Ya ce babban wanda ake zargin, wanda kuma ya jagoranci rabon kudin fansar, shi aka far cafkewa, sannan ya ya tona asirin ragowar.

Mba ya ce an kuma cafke mutum uku tun ranar 28 ga watan Agusta a wani gari da ke tsakanin iyakar Jihar Nasarawa da Jihar Taraba bayan da aka shafe watanni ana neman su.

– An kwace AK-47 guda 26 a hannun masu fasakwaurin

Har wa yau, Mba, ya ce an kamo wasu wadanda ake zargi da laifin saye da sayar da makamai ga masu aikata laifuka a jihohi daban-daban, bayan da jami’an leken asiri suka kai wani samame, bayan samun bayanan sirri.

Mba ya ce an kwato bindigogi kirar AK-47 guda 26, alburusan AK-49 da kuma alburusai kananan bindigogi 14 daga hannun wadanda aka cafke.

Ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotu bayan an kammala bincike.