’Yan sanda sun cafke wani mai sana’ar wankin mota bayan da ya tsere da motar da kwastomarsa ta ba shi ya wanke.
Mutumin da ya gudu da motar ne zuwa Jihar Ogun, ya ce ya fara sana’ar ce a tashar Jimoh, Shasha, Akowonjo, Jihar Legas a ’yan watannin baya kuma yana da shaidar karatu na Diploma daga wata kwalejin kere-kere.
- Yadda korarren direba ya hada baki aka sace matar mai gidansa
- An ceto matar da ’yan uwanta suka kulle watanni 5 a daki
- Gwamnati ta fara biyan ’yan ga-ruwa da direbobi tallafi
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce mai motar ta kai masa ita ya tsaftace ta mika masa makuli.
Kasancewar da ba shi da injin wanke cikin mota sai ya yanke shawarar kai motar wurin masu injin din da ke kusa, amma ya canza shawara a kan hanya kuma ya tsare da motar.
“Yana kan hanyarsa ta zuwa Ibadan ne inda ya yi niyyar sayar da ita ne aka kama shi.
“An tuntubi mai motar, Misis Shofidiya Tosin, wacce ta kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda na Shasha”, inji Oyeyemi.
Oyeyemi ya ce, “Masu sintiri a kan manyan hanyoyi ne suka kama shi ne a kauyen Alakija ta hanyar Olodo da misalin karfe 8.17 a kan babbar hanyar Abeokuta zuwa Ibadan.
“Sun tsayar da motar suka bukaci takardunta amma wanda ake zargin ya kasa samarwa, sakamakon haka aka kai shi Odeda Divisional Headquarters inda DPO Ajayi Williams da kansa ya yi masa tambayoyi kuma ya gano cewa sace motar ya yi”.
Oyeyemi ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Edward Ajogun, ya ba da umarnin a mika lamarin zuwa Legas, inda aka sace motar.