Jami’an bincike sun gano gawarwakin wasu mata biyu da aka binne a ofishin Babban Daraktan Asibitin Kaiama da ke Jihar Kwara, Dokta Abbas Adeyemi.
Daga cikin gawarwakin da aka tono har da ta wata matar mai suna Nofisat Halidu a wani kabari mara zurfi a asibitin a gaban mijinta, kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar.
- Canjin Rayuwa: Mun yi amfani da yajin aikin ASUU —Daliban jami’a
- Ambaliya ta kashe mutum 37 a Adamawa
Adeyemi, wanda a halin yanzu yake tsare, ana zargin shi da laifuka daban-daban na kisan kai.
A watan jiya ne rundunar ‘yan sandan Jihar Edo ta kama Adeyemi kan kisan wani direban tasi mai suna Emmanuel Yobo Agbovinuere.
Dokta Adeyemi wanda ya fito daga Karamar Hukumar Offa ta Jihar Kwara, ana zarginsa da kashe direban tasin ne a ranar 3 ga watan Satumba a garin Benin tare da jefar da gawarsa a unguwar Otofure da ke kan babbar hanyar Benin zuwa Legas.
Likitan, wanda ya kammala karatunsa a Jami’ar Ilorin (Unilorin) a shekarar 2013, bayanai sun ce ya hadu da direban tasin ne wani lokaci a watan Yulin 2022, a wani otal da ya rika yi masa hidima.
Sai dai Paul Odama, sabon Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kwara, ya bayar da umarnin sake gudanar da sabon bincike kan lamarin gawar matar auren da aka tono a ofishin Likitan.
Sanarwar da rundunar ’yan sandan jihar ta fitar ta bayyana cewa, “sabon Kwamishinan ’Yan sanda da ya soma aiki, ya umarci a sake gudanar da sabon bincike kan wata matar aure mai suna Nofisat Abdullahi da aka nema aka rasa tun a ranar 21 ga watan Nuwambar 2021.
“Binciken farko da aka gudanar ya kai mu ga kama wani Dokta Adio Adeyemi Adebowale a Jihar Edo, wanda kuma ya amsa laifin kisan wata budurwarsa da aka nema aka rasa a Ilorin, wani lokaci a bara kuma daga bisani aka gano gawarta a wani jeji inda ya jefarta da ita.
“Wannan lamari ya sanya muka gano cewa Dokta Adeyemi shi ne Babban Darektan Babban Asibitin Kaiama.
“Da muka matsa bincike wanda har ya kai mu zuwa ofishinsa, akwai alamu na sabon siminti a daben wani sashe na ofishin, kuma ana tona wurin sai ga rubabbiyar gawar wata mace a cikin ramin mara zurfi da ko kamanninta ba a iya ganewa.
“Ana tsaka da wannan ne kuma aka bude wani kwandon shara da ke ofishin, sai kuwa aka yi kicibus da gawar wata mai suna Nofisat Halidu wadda mijinta da ’yan uwanta sun dade suna nemanta.
“Sauran ababen da aka samu a ofishin likitan da a yanzu ya shiga hannu sun hada da; wayoyin salula biyu a cikin wata jakar hannu ta mata guda da wasu jakunkunan mata biyu, mayafi (gyale) da kuma dan-kamfai na mata guda daya.”