✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asibitin Benin zai binne gawarwaki 270 da aka rasa ’yan uwansu

Akwai gawarwakin jarirai 201 da ke ajiye a asibiti tun 2023 da na manya 69 da aka kawo tun 2021.

Shugabar sashen kula da gawarwaki na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH), Dakta Ehizogie Egbeobauwaye Adeyemi, ta bayyana cewa asibitin zai binne gawarwaki 270 idan ’yan uwansu suka ƙi zuwa ɗaukarsu nan da makonni shida.

Da take magana da manema labarai a ranar Talata, Adeyemi ta bayyana cewa a cikin akwai yara da jarirai 201 da manya mutane 69.

A cewarta, hukumar asitibitin UBTH a cikin wata sanarwa ta ba da wa’adin makonni shida ga mamallakan gawarwakin da su zo su ɗauke su.

“Akwai gawarwakin jarirai 201 da ke ajiye a asibiti tun 2023 yayin da akwai gawarwakin manya mutane 69 wanda aka kawo su daga Afrilu 2021 zuwa Disamba 2022,” in ji ta.

Adeyemi ta ce asibitin ya yi ƙoƙarin tuntuɓar adireshi da lambobin wayar da masu gawarwakin suka bayar, amma har yanzu ba a iya samun su ko kuma idan an kira ma sai a ji lambobin ba sa aiki.

Sanarwar ta kara da cewa, duk gawarwakin da suka wuce makonni shida za a nemi hanyar binne su ko kuma a bi duk wata hanyar da ta dace.

“Ana sanar da jama’a cewa Hukumar Kula da Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Benin (UBTH), ta kammala shirye-shiryen kwashe duk gawarwakin da ba a kai ga gano masu su ba da suka daɗe a ɗakin ajiyar gawarwaki na Asibitin.”