✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC na taimaka wa masu laifi —Oba na Benin

"Ana zargin maganar wanda ya fi cika wa jami'an aljihu da kudi suke ji

Oba na Benin, Uku Akpolokpolo, Oba Ewuare II, ya zargi jami’an hukumar yaki da masu karya tattalin arzikin kasa (EFCC) da hada baki da masu aikata laifi a Najeriya.

Basaraken ya yi wannan zargi ne a fadarsa lokacin da ya karbi bakuncin sabon Babban Jami’in EFCC mai kula da shiyyar Benin, Effa Okim, wanda ya kai masa ziyarar ban girma.

Oba Ewuare II ya ba da misali da yadda wasu jami’an EFCC a shiyyar suka saki wasu jami’an fadarsa da aka kai karar su kan zargin almundahana.

A cewarsa, duk da kwararan hujjojin da aka gabatar kan wadana ake zargin, jami’an hukumar sun yi wa lamarin rikon sakainar turoso, suka sake su, ba tare da wani kwakkararn mataki ba.

Duk da cewa bai kama sunan wadanda yake zargin ba, Oba na Benin ya shawarci jami’an hukumar da ya zage damtse wajen yaki da almundahana ba sani  ba sabo.

A cewarsa, “Ana zargin maganar wanda ya fi cika wa jami’an aljihu da kudi suke ji.

“Kamar yadda aka san ni da fadin gaskiya, abin da magabacinka ya yi a nan babu dadin ji.

“Me ya sa za su rika yin haka. Wani lokaci muna so mu ba wa EFCC gudummawa amma ba sa ba mu kwarin gwiwa,” in ji basaraken.

A cewarsa, har wasikar korafi ya taba aika wa tsohon shugaban EFCC game da irin tabargazar da jami’an hukumar suke aikatawa a jihar Edo.