Jami’an ’yan sanda sun cafke wani jami’in Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) da wasu mutane biyar bisa zargin satar shanu 164 a Jihar katsina.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin yayin wani baje-kolin masu laifi a hedikwatar ’yan sanda ta Katsina, Kakakin Rundunar, SP Gambo Isah ya ce an cafke mutanen ne a ranar Alhamis lokacin da suke kokarin safarar tirela uku na shanun, da rakiyar jami’in.
SP Gambo ya ce, “Muna ci gaba da bincike a kan lamarin. Muna sane da cewa an sace dimbin shanu a jihohin Katsina da Zamfara, kuma takamaimai ma mun san cewa Zurmi ita ce maboyar bata-garin.
“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba, za mu yi bincike domin mu gano masu shanun na asali tare da tabbatar da cewa dukkan wanda ake zargi daga cikin wadanda muka kama ya gurfana gaban kuliya”, inji kakakin.
Gambo ya kuma yaba da irin hadin kan da suke samu daga gamayyar jami’an tsaron Hukumar Hana Fasa-kwauri ta Kasa ta hanyar musayar bayanan sirri wadanda ya ce su suka taimaka wajen kaiwa ga cafke mutanen.
Jami’in hukumar shige da ficen da aka cafke din ya ce ragowar mutanen da ake zargi ’yan uwansa ne na jini daga Karamar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.
Ya kuma musanta zargin satar shanun, yana mai cewa masu shanun ne ke kokarin kai su garuruwan Potiskum da Buni Yadi na Jihar Yobe domin kauce wa hare-haren ’yan bindiga a Zamfara.
Ya ce ko a baya ya sha raka irin wadannan tirelolin shanun da ke kokarin ficewa daga jihar kafin a kama shi a wannan karon.