’Yan sanda a Jihar Gombe sun kama wani hafsan hukumar gidajen yari da ke aiki a garin Bajoga na Karamar hukumar Funakaye kan zargin sa da yin luwadi da wani karamin yaro.
Da yake gabatar da wanda ake zargin da wasu mutum 14 da ake zargi da laifuffuka daban-daban, kakakin rundunar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce ’yan sandan sun kama wanda ake zargi da aikata luwadin ne bisa rahoton da aka kai musu.
- NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Batun Satar Mazakuta
- Gwamnan Kano ya ba marasa lafiya kyautar N20,000 kowannensu
Amma da wakilin mu yake zantawa da wnada ake zargin, ya bayyana cewa sharri kawai ake masa.
Jami’in gidan gyaran halin ya ce wani mutum ne da kawai bai yarda da mu’amallarsa da mutane ba a garin na Bajoga, ya masa kagen cewa ya yi luwadi da dansa.
Ya ce an je asibiti likita ya gwada yaron da ake zargin sa da shi, amma gwajin bai nuna cewa an yi luwadi da shi ba.
Jami’in ya jaddada cewa bata masa suna aka yi , kuma Allah Zai bi masa hakkinsa.
Ya kara da cewa duk da bai aikata hakan ba kuma yasan luwadi babban laifi ne, yana kira ga masu irin wannan hali da su daina.
Daga nan sai kakakin rundunar ’yan aandan ASP Mahid Mu’azu Abubakar ya ce da zarar sun kammala bincike za su tura wanda ake zargin zuwa kotu.