✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke direban da ya kutsa kai Masallacin Ka’aba

Wata mota ta yi yunkurin kutsawa cikin masallacin Ka’aba inda ta dangane da kofar shiga masallacin ta 89. Kamfanin Dillancin Labaran kasar Saudiyya, ya rawaito…

Wata mota ta yi yunkurin kutsawa cikin masallacin Ka’aba inda ta dangane da kofar shiga masallacin ta 89.

Kamfanin Dillancin Labaran kasar Saudiyya, ya rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Juma’a.

Rahoton ya ce na’urar CCTV ta dauki hoton motar yayin da take yunkurin kutsa kai cikin ginin masallacin.

Sai dai hukumomi sun bayyana cewa babu wanda ya jikkata, sannan kuma an kama direban nan take.

Wasu hotuna sun nuna yadda aka daure hannayensa kafin a fita da shi.

Shingen da aka kama motar za ta kutsa cikin masallacin ba tare da izini ba.

Direban motar da aka kama dan asalin kasar Saudiyya ne, kuma alamu sun nuna cewa yana cikin yanayin tabin hankali.

Jami’an tsaro sun yi awon gaba da shi domin gudanar da bincike a kansa.