✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke dillalin makaman ’yan bindiga a Zamfara

An kama shi da tsabar kudi da zai kai na sayen makamai.

An kama wani dillalin makaman ’yan bindiga tare da wasu ’yan fashi a Jihar Zamfara.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Abutu Yaro ya ce an kama dillalin makaman ne suna cikin cinikin bindiga kirar AK-47 daga wani dan bindiga a daji.

“Jami’anmu masu sintiri sun yi nasarar kama wani mutum da tsabar kudi Naira miliyan daya da dubu saba’in.

“A yayin da muka titsiye shi ne ya bayyana cewa an ba shi kudin ne ya kai wa wani a Karamar Hukumar Zurmi.

“Bisa hakan ne jami’anmu suka kama wani gawurtaccen dan ta’adda da bindiga kirar AK-47 da harsasai, ana kuma kokarin kamo abokan sana’ar tasu,’’ inji Kwamishinan ’Yan Sandan.