Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da satar janareta da batir din injin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a wani masallaci.
Kakakin rundunar, Mansir Hassan, ya ce jami’an tsaro sun kama daya daga cikin wadanda ake zargin ne a unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Hunkuyi.
Ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa an kama shi ne sakamakon rashin yardar jama’a da motsinsa a kusa da masallacin.
“A lokacin da ake masa tambayoyi, ya amsa laifin satar janareta da batir mai amfani da hasken rana a masallatan kauyukan Hunkuyi da Nahuce.
- Kwana 7 na kasa barci saboda jiran hukuncin Kotun Koli —Bala Mohammed
- Abba ya nada Gawuna da Ganduje a Majalisar Dattawan Kano
“Ya bayyana cewa ya sayar da kayan da ya sata ga wani Mansir Umar wanda shi ma muka kama shi ba tare da bata lokaci ba.
“An gano wasu abubuwan nunin kuma ana ci gaba da bincike.
“Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike.”