Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) sun tsallake rijiya da baya da raunukan harbin bindiga bayan da ɓata-gari suka buɗe musu wuta a lokacin da suka kama miyagun ƙwayoyi a Yankin Banban Birnin Tarayya.
Mutum uku daga cikin jami’an sun samu raunuka an harbi, ɗaya a haƙari, biyu a gadon baya da kafafunsu, a yayin harin da aka kai musu a unguwar Jahi, bayan sun kama wasu miyagun ƙwayoyi a ranar Alhamis.
Kakakin NDLEA na ƙasa, Femi Babafemi, ya bayyana cewa an kwantar da jami’an guda uku a asibiti saboda raunukan harbin bindiga da suka samu.
“Lamarin ya faru ne a lokacin da tawagar jami’an NDLEA, bisa bayanan sirri, suka kai samame wani kwangon gini a yankin NNPC da ke unguwar Jahi inda aka ƙwato kwalaben codeine guda 74, codeine ta ruwa lita 10, gram 48 na tramadol mai milligram 225, da kilogiram 4.9 na skunk, wani nau’in tabar wiwi, da kuma wayoyin android guda biyar.
- ’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun lashe ɗan bindiga a Edo
- Makarantar Bare: Shekara 20 dalibai na karatu a matsanancin yanayi
“Yayin da tawagar NDLEA ke hanyarsu ta fita daga wurin kuma an kai musu harin bindiga,” in ji Babafemi a cikin sanarwar da ya fitar washegari da daddare.
Babafemi ya ce, an fara ba da kulawar gaggawa ga jami’an da suka ji rauni a asibitin ’yan sanda da ke Garki Area 1 kafin a mayar da su Babban Asibitin Abuja domin ƙarin kulawa.
Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya), ya yaba wa ma’aikatan asibitin ’yan sanda bisa ga agajin gaggawar da suka bayar.
Ya kuma gode wa Shugaban Asibitin Ƙasa, wanda shi da kansa ya tuntube shi domin ya kula da jinyar jami’an da suka ji rauni.
Shugaban NDLEA, wanda ke Kano a kan ayyukan hukuma, ya kuma yi magana ta waya da jami’an da suka ji rauni domin yi musu fatan samun sauƙi cikin gaggawa.
Ya ba su tabbacin cewa hukumar za ta yi amfani da duk wata hanya da take da ita kuma za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin gano waɗanda ke da alhakin kai musu harin.