✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An buqaci al’umma su qaurace wa kayan maye

An kirayi mutane, musamman wadanda ke mu’amala da abubuwan sa maye da su nisanta kansu daga harkar saboda illolin da ke tattare da ita. Babban…

An kirayi mutane, musamman wadanda ke mu’amala da abubuwan sa maye da su nisanta kansu daga harkar saboda illolin da ke tattare da ita.

Babban limamin masallacin Juma’a na barikin ’yan sanda da ke Yola Jihar Adamawa, DSP Ahmad Suleiman ne ya bayyana haka, a lokacin da yake zantawa da manema labarai. Ya ce yin maye shi ne silar duk wata fitina da ke haddasa duk wata masifa ko rikici a tsakanin al’umma saboda haka ya kamata a dauki mataki domin magance shi.

Suleiman ya shawarci matasa da su nisanta kansu da irin wadannan dabi’u na shaye-shaye, kasancewar su ne shuwagabannin gobe. Ya kuma kirayi iyaye da su kula da irin tarbiyyar da suke bai wa yaransu.

Ya qara da cewa, ya kamata hukumomin tsaro su qara himma wajen magance matsalar shaye-shaye a tsakanin al’umma baki daya. Sannan ya buqaci al’umma su kasance masu yin addu’o’i ga shugabanni da qasa baki daya domin samun zaman lafiya.