✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci shugabanin addini su daina aibanta juna

Wani Dattijo a Jihar Gombe, Malam Magaji Musa Miringa ya yi kira ga shugabanin addinin Musulmi da na Kirista su daina zargin juna a kan…

Wani Dattijo a Jihar Gombe, Malam Magaji Musa Miringa ya yi kira ga shugabanin addinin Musulmi da na Kirista su daina zargin juna a kan ta’addanci.

Malam Magaji ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gombe, inda ya ce a kasar nan shugabanin addinan nan biyu sun jima suna zargin junansu a kan ta’addanci tun lokacin rikicin Marwa Maitatsine, a zamanin mulkin Shagari.

Ya ce zargin shi ne Musulmi suna cewa Maitatsine Kirista ne, Kiristoci suna cewa Musulmi ne har aka zo kan rikicin Boko Haram inda hakan ya kara farraka kan al’umma, nan ma shugabanin suka sake zargin juna har aka zo aka gane a cikin ’yan Boko Haram akwai Musulmi akwai Kirista.

Ya kuma yi kira ga shugabannin addinan su zauna a bisa tebur su warware wannan matsalar, su daina zargin kowane bangare.

Dattijon  ya nemi mabiya su yi wa shugabanni biyayya muddin aka zauna aka samar da matsaya don Allah ne Ya ce bin shugabani bin Allah ne, muddin ba su kauce shari’a ba.

Daga nan sai ya ce su ma ’yan siyasa da jami’an tsaro suna da rawar takawa domin idan suka zauna za su samar da mafita da za ta ceto kasar nan daga halin rikicin da ake fama da shi.

Sannan ya bai wa gwamnati shawarar ta tashi tsaye a matsayinta na hukuma, don hukunta duk wanda yake da hannu a kowanne irin rikicin da yake faruwa a kasar nan.