Kungiyar Hada-Kan Jama’a don Tabbatar da Zaman Lafiya (Community Peace Partnership- CPP), ta bukaci makiyaya da manoma su kawo karshen kashe-kashen juna da lalata dukiyoyi da suke yi a tsakaninsu a fadin kasar nan.
Alhaji Iliyasu Musa, Shugaban kungiyar a karamar Hukumar Jama’a ya yi wannan kira a wajen taron manema labarai da kungiyar ta kira a sakatariyar karamar hukumar da ke garin Kafanchan, don murnar zagayowar Ranar Zaman Lafiya ta Duniya da Majalisar dinkin Duniya ta ware a farkon watan Oktoban kowacce shekara.
Shugaban, ya ce dole sai an yaki fatara da yunwa, tare da cin hanci da rashawa da nuna kabilanci da wariyar addini kafin zaman lafiya ya samu tabbata a cikin al’ummar da ke zaune da juna a wannan kasar.
A lokacin da yake bayar da misali da rikicin kwana-kwanan nan da ya auku a wasu sassa na Kudancin Kaduna tsakanin manoma da makiyaya wanda ya samo asali daga garin Ninten Godogodo, ya kuma yadu zuwa wasu sassa da suka hada da Gada Biyu da Akwa da Ungwan Anjo da Golkofa, ya ce an yi asarar rayukan mutum 40 tare da lalata gidaje da dabbobi da kayan amfanin gona da suka kai na miliyoyin Naira. Ya bayyana cewa hakan ba karamar koma baya ba ce a gare su da kuma Jihar Kaduna baki daya.
Lokacin da yake bayyana taken taron na bana mai suna ‘Aza Harsashin Zaman Lafiya’, Shugaban, ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kaduna da ta karamar Hukumar Jama’a su samar da isassun jami’an tsaro a kan iyakokin garuruwan da irin wannan rikici ke yawan faruwa, sannan a raba mutanen yankin da makaman da suke hannayensu tare da samar da abubuwan more rayuwa da ayyukan yi ga matasa a wani mataki da kungiyar ke gani zai iya magance aukuwar irin wannan tashin hankali a nan gaba.
Sai ya yi kira ga manoma da makiyaya da ke yankin Kudancin Kaduna su yi hakuri su yafe wa juna tare da yin watsi da jita-jita kuma su yi kokarin dawo da zaman lafiya da aka sansu da shi tuntuni, inda ta kai Fulani makiyaya na jin harsunan kabilun da suke zaune tare da su kamar yadda su ma kabilun ke yin Fulatanci . Ya bukaci su dore da hakan, gudun kada irin wannan rikici ya ci gaba da yaduwa zuwa wasu sassan Kudancin Kaduna wanda a karshe yana iya rikidewa daga rikicin manoma da makiyaya zuwa rikicin addini da kabilanci da ba a fatan sake aukuwar irin haka nan gaba a yankin.
An bukaci makiyaya da manoma su zauna lafiya da juna
Kungiyar Hada-Kan Jama’a don Tabbatar da Zaman Lafiya (Community Peace Partnership- CPP), ta bukaci makiyaya da manoma su kawo karshen kashe-kashen juna da lalata dukiyoyi…