✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci Bankin Masana’antu ya rage kudin ruwa

An yi kira ga gwmanatin tarayya da ta rage kudin ruwa da Bankin Kula da Masana’antu yake sanyawa a kan karbar bashi, hakan shi zai…

An yi kira ga gwmanatin tarayya da ta rage kudin ruwa da Bankin Kula da Masana’antu yake sanyawa a kan karbar bashi, hakan shi zai taimaka wajen kokarin da gwamantin ke yi na farafado da masana’antu a fadin kasar nan, kamar yadda wani dan kasuwa ya bukata.
dan kasuwar wanda kuma darakta ne a Kamfanin kaura Biscuit and Macroni Limited da ke Jihar Kano, Alhaji Shitu Sani Marshall ya yi wannan kira ne a tattaunawar da ya yi da Aminiya a Kano.
Shitu Marshal ya bayyana cewa a baya akwai kimanin masana’antu 300 a jihar, wadanda a yanzu duk sun durkushe sakamakon rashin tsayayyiyar wutar lantarki da kuma yawan kudin ruwa idan sun karbi bashi da kuma rashin yanayi mai kyau na gudanar da aiki.
“Idan har gwamnati za ta rage kudin ruwa da Bankin Talalfawa Masana’ntu yake sanya wa ga masu karbar ba shi, to babu ko shakka masu masana’antu wadanda suka durkushe za su samu farfado su ci gaba da gudanar da ayyukansu. A da jihar nan kawai muna da masana’antu fiye da da 300 a yanzu kuwa wadanda ke aiki ba su fi guda 30 ba.
A yanzu haka masa’antun sun zama kangwaye babu komai a cikin sai beraye da gafiyoyi,” inji shi.
Ya bayyana cewa idan har masana’antu suka dawo bakin aiki gadan-gadan, to za a samu raguwar zaman banza da shaye-shaye tsakanin matasan jihar wadanda a kullum suke shiga ayyukan sakamakon rashin aikin yi.
Da yake karin haske game da alfanun da ke akwai a cikin farfado da masana’antun shi ne gwamnati za ta rika samun kudin shiga daga masana’antu.
Har ila yau, Alhaji Shitu ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta kara samar da wurin da za a yi wasu masana’antu a jihar, kasancewar wadanda ake da su a jihar sun yi kadan.
Ya ce “idan kika dubi wuraren da masana’antunmu suke a Kano inda ya hada da Chalawa da Bomap da Sharada za ki ga cewa sun yi kadan duba da yawan jama’ar da ke jihar.”
Akwai bukatar gwamnati ta sake samar da wadansu wuraren don Alhaji Shitu ya yi wa jama’ar kasar nan albishir samun ingantattun kayayyaki na gida wadanda za su iya  gogayya da na kasashen ketare.